Sunday, June 2, 2024

Real Madrid ta lashe Champions League na goma sha biyar (15) a wasan karshe.


 


Real Madrid ta lashe Champions League na goma sha biyar (15) ranar Asabar daya (1) ga watan Yuni a Wembley, wadda ta buga wasan karshe na 18 a gasar.

Kungiyar dake Santiago Bernabeu ta doke Borussia Dortmund 2-0, wadda tuni ta dauki La Liga na bana, kuma na 36 a tarihi.


Wanna shi ne karon farko da Real Madrid da Borussia Dortmund suka fafata a wasan karshe a babbar gasar tamaula ta Turai, amma karo na goma sha biyar (15) da za su kece raini.

Real Madrid ce kan gaba a yawan zuwa karawar karshe a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, kuma ita ce kan gaba a yawan lashe kofin a tarihi.


Real ta fara daukar kofin farko zuwa na biyar tare da jagorancin Di Stefano tsakanin 1956 zuwa1960Real Madrid.

Kungiyoyin da ta doke a lokacin sun hada da Reims, 4-3 da Fiorentina, 2-0 da kuma Milan 3-2 da Stade de Reims

2-0 da kuma Eintracht Frankfurt 7-3.

Bayan da Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Benfica da kuma Inter a 1962 da kuma 1964, daga nan ta dauki na shida da ake kira La Sexta a 1966 bayan nasara a kan Partizan 2-1.


A 1981, Madrid ta kasa daukar Champions League, bayan rashin nasara a hannun Liverpool.

Daga lokacin kuma ta dunga lashe dukkan karawar da ta kai wasan karshe ta kuma doke Juventus ta dauki La Séptima a Amsterdam a 1998, bayan cin 1-0.

Haka kuma ta dauki na La Octava bayan dokeReal Madrid


Valencia 3-0 a Paris, sai ta daga La Novena a wasan da ta doke Bayer Leverkusen 2-1 a Glasgow a 2002, shi ne lokacin da Zidane ya ci kwallo mai kayatarwa.

A kakar 2014 tare da Ancelotti a kan ragama ta dauki La Decima a Lisbon da cin 4-1 har da kwallo mai kayatarwa da Ramos ya ci.

A 2016 Real Madrid ta doke Atletico ta dauki La Undecima a birnin Milan.

Haka kuma Real Madrid ta dauka a 2017, wato La Duodecima a birnin Cardiff bayan nasara a kan Juventus da cin 4-1.

A 2018, Real ta doke Liverpool da cin 3-1 ta lashe La Decimotercera.

Sai kuma a 2022, Real Madrid ta kara yin nasara a kan Liverpool da cin 1-0 a Paris ta dauki na 14 jimilla, wato La Decimocuarta.

A 2024, Real Madrid ta dauki Champions League na goma sha boyar (15) jimilla.

Jerin wadanda suka lashe Champions League

Real Madrid ta lashe Champions League na goma sha biyar (15) a wasan karshe.

  Real Madrid ta lashe Champions League na goma sha biyar (15) ranar Asabar daya (1) ga watan Yuni a Wembley, wadda ta buga wasan karshe na ...